Manufar Dan Bello
Manufar Dan Bello - Ƙarfin Jama’a, Sabuwar Duniya
1. Su Waye Mu?
Mu ne ‘ya’yan ƙasa. Muryar waɗanda aka manta da su. Wadanda suka ƙi yarda da zalunci. Masu burin ganin maza sun dena durkusawa domin a basu shinkafa, kuma mata sun dena roko domin a mutunta su. Mu ba ’yan siyasa ba ne, kuma mu ba masu iko ba ne.
Mu jama’a ne. Kuma mun farka.
2. Abin da Muke Ƙyama
• Muna ƙyamar cin zarafi da talauci da ake ɗora wa talakawa.
• Muna ƙyamar rarrabuwar kawuna bisa kabila da addini.
• Muna ƙyamar shiru a lokacin zalunci.
• Muna ƙyamar tsarin da yake ba mu wuya a rayuwarmu, yayin da manya ke cin arziki.
3. Abin da Muke Ƙuduri
• Mu kafa al’umma mai adalci da daidaito.
• Mu farfado da al’adunmu, ba kamar kayan wasan kwaikwayo ba, amma a matsayin makami.
• Mu dawo da darajar malamai, manoma, da masu fasaha.
• Mu tashi tsaye mu karɓi ikon da ke hannun masu cutar da mu.
4. Alkawarin Mu
Ba mu yi alkawarin samun sauƙi ba.
Ba mu yi alkawari jin daɗi ba.
Amma mun yi alkawarin gwagwarmaya.
Mun yi alkawarin karewa wajen gina sabuwar duniya da ke da daraja ga kowa.
Kalamai Na Ƙarshe
“Idan za mu mutu, to mu mutu da hannu a sama, ba da hannu cikin roƙo ba da bara ba.”
“Ba ma neman shiga a wajen kowa —zuwa muka yi mu girgije teburin.”
“Ƙarfin Jama’a, Sabuwar Duniya!”
Wannan page din mune don yada manufar Dan Bello:
https://www.facebook.com/profile.php?id=61576953244201
Wannan kuma group ɗin mu ne domin tattaunawa da jin ra'ayinku da daukar kokenku:
https://facebook.com/groups/1977341549466752/
Mun Gode.
Comments
Post a Comment